A Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, an yanke wa mutum biyu hukuncin ɗaurin rai da rai bayan samunsu da laifin samar wa mayaƙan ƙungiyar Boko Haram tallafin kayan aiki da sufuri.

Kotun ta kuma ƙara musu hukuncin ɗaurin shekaru 20 kowannensu bisa laifin ɓoye bayanai daga hukumomi. Rahoton ya ce mutanen biyu, waɗanda suka fito daga Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, sun amsa laifukan da ake tuhumarsu da su.

A wata shari’a dabam da aka gudanar a Jihar Kebbi, da ke arewa maso yammacin ƙasar, an yanke wa wasu mutum 19 hukuncin ɗauri na tsawon shekaru daban-daban kan laifukan da suka shafi ta’addanci.

Daga cikin waɗanda aka yanke wa hukunci akwai wani ɗan ƙasar China mai suna Ripin Liu da wasu mutum 10, waɗanda aka same su da laifin mallakar bindigogi ba bisa ƙa’ida ba. An yanke wa Liu hukuncin ɗaurin shekaru shida, tare da damar biyan tara a madadin zaman gidan yari.

Haka kuma, kotun ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin ɗaurin shekaru 45 kowannensu bayan samunsu da laifukan ta’addanci, samar da tallafin kayan aiki ga ƙungiyar masu ɗauke da makamai da kuma haɗa baki domin aikata ayyukan ta’addanci.

Sauran mutum shida sun samu hukuncin ɗaurin shekaru uku zuwa takwas saboda laifukan lalata kayayyakin gwamnati da satar wayoyin lantarki.

Tun bayan fara gudanar da shari’o’in masu zargin aikata laifukan ta’addanci a watan Oktoban 2017, rahoton ya ce an samu hukuncin ɗauri kan fiye da mutum 1,721 da aka same su da laifuka masu alaƙa da ta’addanci.

Ana gudanar da irin waɗannan shari’o’i ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin hukumomin Najeriya na gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifukan ta’addanci a gaban kotu.