Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya kusanci dala 110 kan kowace ganga, a karon farko tun daga watan Mayun 2026, sakamakon fargabar ƙarin tsanantar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.
An zaɓi Najeriya a matsayin mamba a Majalisar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHRC) na wa’adin shekarun 2027 zuwa 2029, bayan ta samu ƙuri’u 172 cikin ƙuri’u 181 da aka kaɗa a Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya.
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama mutane 1,860 tare da ƙwace kilogiram 5,409.814 na miyagun ƙwayoyi a Jihar Kano tsakanin Janairu da Satumba 2026.
Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci na Iran (IRGC) sun bayyana cewa ƙasar ta samu sabbin manyan makamai bayan yaƙin da ta yi da Amurka da Isra’ila, tare da gargaɗin cewa za ta mayar da martani mai tsanani idan aka sake kai mata hari.
Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya shawarci Najeriya da kada ta dawo da tsarin tallafin man fetur, inda ya buƙaci gwamnati ta mayar da hankali wajen tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi domin rage tasirin hauhawar farashin makamashi.
Akalla mutane biyu sun mutu, yayin da wasu 21 suka jikkata sakamakon hare-haren sama da Rasha ta kai kan birnin Kyiv, babban birnin Ukraine, inda aka samu katsewar wutar lantarki a sassa daban-daban na birnin.
Shugabannin ƙasashen duniya sun ci gaba da aika saƙonnin fatan samun sauƙi cikin gaggawa ga Paparoma Leo, bayan an yi masa tiyatar da aka ce an cire wani ɓangare na huhunsa na dama a birnin Rome.
Lauyoyin Isa Ali Pantami sun bai wa INEC wa’adin kwanaki uku ta sanya sunansa cikin jerin ’yan takarar gwamnan Gombe na PDP a zaɓen 2027, ko kuma su garzaya kotu
An ji wata babbar ƙarar fashewa a filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Riyadh, babban birnin Saudiyya, a daidai lokacin da ake samun rahotannin ƙaruwa da hare-haren makamai masu linzami da ake dangantawa da ƙungiyar Houthi ta Yemen. Ya zuwa yanzu, hukumomin Saudiyya ba su tabbatar da cewa an kai hari a filin jirgin saman ba. Sai dai rahotannin farko sun nuna cewa an fara kwashe mutane daga filin jirgin. Kamfanonin jiragen sama na Etihad Airways da Qatar Airways sun soke wasu jirage da dama da za su tashi zuwa Riyadh, ciki har da wasu da aka tsara gudanarwa har zuwa ranar Litinin. Wannan na zuwa
Gwamnatin Ghana ta dakatar da aiwatar da dokar da ta haramta wa’azi da talla a cikin motocin haya da na jama’a yayin da suke tafiya. Sabuwar dokar zirga-zirgar ta tanadi hukuncin ɗaurin watanni takwas a gidan yari ko tara da ta haura dala 52 ga duk wanda ya karya dokar. Rahoton BBC da aka fitar kan dokar ya janyo muhawara a Ghana, musamman dangane da tasirinta ga ’yancin addini da bayyana ra’ayi. Mai magana da yawun gwamnatin Ghana, Felix Kwakye Ofosu, ya shaida wa BBC a ranar Juma’a cewa akwai buƙatar sake nazarin dokar, bayan da wasu shugabannin addinai suka nuna damuwa kan yadda za a aiwata
Kasar Sin ta gabatar wa Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) da ke birnin Vienna na Austria samfurin ƙasa da aka debo daga ɓangaren nesa na Wata, a wani muhimmin mataki na binciken sararin samaniya. An debo samfurin ne a yayin binciken da kumbon Chang’e-6 ya gudanar a shekarar 2024. China ta ce samfurin zai ci gaba da kasancewa a cibiyar MDD domin a riƙa baje kolinsa ga jama’a. An gudanar da bikin miƙa samfurin ne ƙarƙashin taken “Daga Wata zuwa Duniya: Makomar Ci Gaba Ta Bai Ɗaya ga Kowa” , inda jami’an diplomasiyya, jami’an MDD, masana kimiyya da wakilan ƙungiyoyin duniya suka halarta. Samfurin, wa
Amurka na fuskantar ƙarancin wasu muhimman makamai sakamakon tsadar yaƙin da take yi da Iran, a cewar wani rahoton sa ido kan ayyukan Ma’aikatar Tsaron Amurka, Pentagon. Rahoton, wanda aka gabatar wa Majalisar Dokokin Amurka, ya ce tsakanin 28 ga Fabrairu zuwa 30 ga Yuni , rundunar Operation Epic Fury (OEF) ta kashe kimanin dala biliyan 33.4 , ciki har da dala biliyan 22.3 da aka kashe wajen makamai a wannan lokacin. Rahoton ya ce yawan kuɗaɗen da aka kashe wajen gudanar da Operation Epic Fury ya haifar da ƙarancin wasu muhimman kayayyakin yaƙi, tare da bayyana ƙalubalen da masana’antun kera m
Amurka na fuskantar ƙarancin harsasai sakamakon yaƙin da take yi da Iran , kamar yadda Ofishin Babban Sufeto Janar na Ma’aikatar Tsaron Amurka (Department of Defense) ya tabbatar a ranar Litinin. Wannan ya saɓa da ikirarin Shugaba Donald Trump na cewa Amurka na da isassun kayan yaƙi a hannunta. A wani rahoto na farko irinsa da aka tilasta wa ofishin gabatarwa ga Majalisar Dokokin Amurka, Babban Sufeton ya bayyana cewa tsakanin ranar 28 ga Fabrairu zuwa 30 ga Yuni, Operation Epic Fury ta kashe kimanin dala biliyan 33.4, ciki har da dala biliyan 22.3 da aka kashe wajen amfani da makamai da harsa
Rundunar sojin Uganda ta musanta zargin cewa ta tsoma baki cikin rikicin da ya kunno kai kan wanda zai gaji marigayi Sarki Oyo Nyimba na masarautar Tooro. Mai magana da yawun rundunar ya ce sojojin ba su janye jami'an da ke gadin masarautar ba, kuma ba su tsare iyalan marigayi sarkin a cikin fadar ba. Ya ce rundunar ta ƙara tsaurara matakan tsaro a fadar ne gabanin jana'izar sarkin da za a gudanar ranar Asabar, saboda ana sa ran dubban mutane za su halarta. Jami'in ya kuma ce fadar tana kusa da iyakar gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, yankin da ke fama da matsalolin tsaro, don haka ake
Gwamnatin Kenya ta bai wa baƙin haure da ke gudanar da ƙananan sana’o’i a ƙasar wa’adin kwanaki 90 su mallaki takardun zama, izinin aiki da kuma lasisin gudanar da kasuwanci. Kakakin Fadar Shugaban Ƙasar, Hussein Mohammed, ya ce za a gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar ofisoshin jakadancin ƙasashen da abin ya shafa, domin bai wa baƙin hauren damar daidaita takardunsu da harkokin kasuwancinsu cikin tsari. Ya ce gwamnati za ta yi amfani da kwanaki 90 masu zuwa wajen gudanar da aikin, kuma bayan cikar wa’adin za a fara tsaurara aiwatar da dokokin shige da fice. Matakin ya biyo bayan umarnin
Aƙalla mutum biyar sun mutu, yayin da wasu biyar suka samu munanan raunuka bayan wani jirgin dakon kaya na kamfanin Amazon Air ya kauce daga titin saukar jirage yayin da yake ƙoƙarin sauka a filin jirgin sama na Miami International Airport da ke Amurka. Jirgin, samfurin Boeing 767-300 , ya yi hatsarin ne jim kaɗan kafin ƙarfe biyu na rana agogon ƙasar, wato ƙarfe 19:00 agogon GMT, bayan da ya tashi daga filin jirgin sama na Luis Muñoz Marín da ke San Juan, Puerto Rico. Rahotanni sun ce jirgin ya kuma bugi wasu motoci da ke kusa da wurin da hatsarin ya afku. Kamfanin Amazon ya bayyana cewa yana
Iran ta gargadi Koriya ta Kudu kan duk wani shiri na tura dakarunta ko shiga ayyukan soji a Tekun Fasha da mashigar Hormuz, tana mai cewa hakan zai haifar da mummunan sakamako . Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei , ne ya yi gargadin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X da harshen Koriya. Baghaei ya ce Iran za ta ɗauki duk wani kasancewar sojojin Koriya ta Kudu ko shiga ayyukan soji a yankin a matsayin goyon bayan Amurka , tare da yin gargadin cewa hakan zai haifar da mummunan sakamako. Gargadin na Iran na zuwa ne yayin da gwamnatin Koriya ta Kudu ke nazarin
Fiye da mutane 900 ne suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila a Zirin Gaza tun farkon wannan shekara, duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma, a cewar sabbin alkaluman Ma’aikatar Lafiya ta Gaza. Ma’aikatar, wadda ke karkashin Hamas, ta ce jimillar Falasɗinawan da suka rasa rayukansu a Gaza tun bayan ayyana tsagaita wutar a ranar 10 ga Oktoba , ta haura 1,300 , ciki har da yara 301 . Isra’ila da Hamas sun amince da tsagaita wutar ne bayan bangarorin biyu sun karɓi shirin zaman lafiya mai maki 20 da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya gabatar. Shirin ya tanadi dakatar da dukkan ayyukan soj