Amurka na fuskantar ƙarancin harsasai sakamakon yaƙin da take yi da Iran , kamar yadda Ofishin Babban Sufeto Janar na Ma’aikatar Tsaron Amurka (Department of Defense) ya tabbatar a ranar Litinin.
Wannan ya saɓa da ikirarin Shugaba Donald Trump na cewa Amurka na da isassun kayan yaƙi a hannunta.
A wani rahoto na farko irinsa da aka tilasta wa ofishin gabatarwa ga Majalisar Dokokin Amurka, Babban Sufeton ya bayyana cewa tsakanin ranar 28 ga Fabrairu zuwa 30 ga Yuni, Operation Epic Fury ta kashe kimanin dala biliyan 33.4, ciki har da dala biliyan 22.3 da aka kashe wajen amfani da makamai da harsasai.
Rahoton ya ce: “Yawan makaman da aka yi amfani da su a Operation Epic Fury ya haifar da gibin makamai a ma’ajiyar dabarun soji, tare da bayyana matsalolin da ke cikin masana’antun kera makamai wajen sake samar da harsasai.”
Operation Epic Fury shi ne sunan da Amurka ta bai wa yakin haɗin gwiwa da Isra’ila, wanda rundunar sojin Amurka ta Central Command ta ce an gudanar da shi ne domin “lalata karfin Iran na amfani da karfin soji wajen aiwatar da manufofinta.”
