Kasar Sin ta gabatar wa Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) da ke birnin Vienna na Austria samfurin ƙasa da aka debo daga ɓangaren nesa na Wata, a wani muhimmin mataki na binciken sararin samaniya.
An debo samfurin ne a yayin binciken da kumbon Chang’e-6 ya gudanar a shekarar 2024. China ta ce samfurin zai ci gaba da kasancewa a cibiyar MDD domin a riƙa baje kolinsa ga jama’a.
An gudanar da bikin miƙa samfurin ne ƙarƙashin taken “Daga Wata zuwa Duniya: Makomar Ci Gaba Ta Bai Ɗaya ga Kowa” , inda jami’an diplomasiyya, jami’an MDD, masana kimiyya da wakilan ƙungiyoyin duniya suka halarta.
Samfurin, wanda aka samo daga ɓangaren nesa na Wata mai tazarar kusan kilomita 380,000 daga Duniya , an miƙa shi ga cibiyar harkokin diplomasiyya ta duniya a matsayin wata alama ta ci gaban binciken kimiyya da haɗin gwiwar ƙasashe.
Tarihin Chang’e-6
A shekarar 2024 , aikin binciken sararin samaniya na China mai suna Chang’e-6 ya samu nasarar dawo da samfurin ƙasa mai nauyin gram 1,935.3 daga ɓangaren nesa na Wata.
Wannan ya kasance karo na farko a tarihin ɗan Adam da aka samu nasarar dawo da samfurin ƙasa daga wannan ɓangaren Wata zuwa Duniya.
Masana kimiyya na ganin irin waɗannan samfurori za su iya taimakawa wajen ƙara fahimtar tarihin samuwar Wata da kuma yadda tsarin sararin samaniya ya sauya cikin shekaru biliyoyin da suka gabata.
Miƙa samfurin ga MDD na kuma zama wata alama ta yadda binciken sararin samaniya zai iya zama wani fage na haɗin gwiwar ƙasashe da musayar ilimin kimiyya .
