MF ta bayyana cewa tallafin man fetur na bai ɗaya yana jawo wa gwamnati kashe kuɗaɗe masu yawa, yayin da galibi masu samun kuɗaɗen shiga masu yawa suka fi cin gajiyar tsarin fiye da masu ƙaramin ƙarfi.
Asusun ya kuma yi gargaɗin cewa dawo da tallafin na iya ƙara matsin lamba kan kasafin kuɗin gwamnati, musamman a lokacin da kuɗin rance ke ƙaruwa.
A maimakon haka, IMF ta ba da shawarar cewa Najeriya ta rungumi tsarin tallafi da aka tsara musamman domin taimaka wa gidaje masu ƙaramin ƙarfi da waɗanda hauhawar farashin makamashi ta fi shafa.
Daraktan Sashen Harkokin Kasafin Kuɗi na IMF, Rodrigo Valdés, ne ya bayyana wannan matsaya yayin wani taron manema labarai kan rahoton sa ido kan harkokin kasafin kuɗi.
An gudanar da taron ne a gefen taron shekara-shekara na IMF da Bankin Duniya na shekarar 2026, wanda ake gudanarwa a Bangkok, babban birnin Thailand.
Shawarar ta sake buɗe muhawara kan yadda Najeriya za ta daidaita buƙatar rage tsadar rayuwa da kuma kiyaye kuɗaɗen gwamnati, musamman yayin da farashin man fetur da sauran kayayyakin masarufi ke shafar rayuwar al’umma.
