Amurka na fuskantar ƙarancin wasu muhimman makamai sakamakon tsadar yaƙin da take yi da Iran, a cewar wani rahoton sa ido kan ayyukan Ma’aikatar Tsaron Amurka, Pentagon.

Rahoton, wanda aka gabatar wa Majalisar Dokokin Amurka, ya ce tsakanin 28 ga Fabrairu zuwa 30 ga Yuni , rundunar Operation Epic Fury (OEF) ta kashe kimanin dala biliyan 33.4 , ciki har da dala biliyan 22.3 da aka kashe wajen makamai a wannan lokacin.

Rahoton ya ce yawan kuɗaɗen da aka kashe wajen gudanar da Operation Epic Fury ya haifar da ƙarancin wasu muhimman kayayyakin yaƙi, tare da bayyana ƙalubalen da masana’antun kera makamai ke fuskanta wajen cike gibin kayayyakin da ake amfani da su.

Asarar jiragen yaƙi

Rahoton ya kuma bayyana irin asarar kayan aikin soji da Amurka ta yi a yayin yaƙin.

A cewarsa, jiragen yaƙin F-15 guda huɗu sun lalace, yayin da wani jirgin F-35 ya yi hatsari. Haka kuma, manyan jiragen ɗaukar mai na KC-135 guda bakwai sun lalace, yayin da aka harbo jirage marasa matuƙa na MQ-9 Reaper guda 30 .

Rahoton ya ce hare-haren sun kuma janyo babbar asarar kayan aikin soji da wasu muhimman kayayyakin more rayuwa na Amurka a yankin.

Trump ya yi watsi da damuwar ƙarancin makamai

Shugaban Amurka, Donald Trump , ya yi watsi da damuwar da ake nunawa kan ƙarancin makamai.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social ranar Litinin, Trump ya ce masana’antun Amurka na samar da makamai masu inganci da na musamman fiye da kowane lokaci a tarihin ƙasar.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa ƙarancin wasu makamai masu linzami masu cin dogon zango da makaman kare sararin samaniya ya shafi yadda sojojin Amurka ke gudanar da ayyukansu a Iran.

An kuma ruwaito cewa sojojin Amurka sun yi amfani da kusan kashi 80 cikin 100 na makamansu na THAAD , waɗanda ake amfani da su wajen kare wurare daga hare-haren makamai masu linzami.

Hare-haren Iran sun lalata sansanonin Amurka

A cikin sa’o’i 24 na farko bayan fara yaƙin, Rundunar Tsakiyar Amurka, CENTCOM , ta kai hare-hare kan wurare sama da 1,000 , sai dai adadin hare-haren ya ragu a watannin da suka biyo baya.

Hukumar sa ido ta ce hare-haren Iran sun lalata ɗaruruwan wurare a sansanonin Amurka da ke Kuwait, Bahrain, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Saudiyya, Iraƙi, Oman da Jordan .

Ta ce ba a haɗa kuɗaɗen sake gina wuraren da suka lalace cikin waɗannan ƙididdigar ba, yayin da jami’an Amurka ke ci gaba da tantance wuraren da za a sake ginawa da kuma hanyoyin samun kuɗin gudanar da ayyukan.