AMMASCO RADIO NEWSROOM

security

Najeriya Ta Yanke wa Mutum 21 Hukuncin Ɗauri Kan Laifukan Ta’addanci

Najeriya ta ci gaba da gudanar da shari’o’in masu zargin aikata laifukan ta’addanci, inda a ranar 16 ga Oktoba aka yanke wa mutum 21 hukuncin ɗauri kan laifuka daban-daban da suka shafi ta’addanci, ciki har da wani ɗan ƙasar China, kamar yadda jaridar The Sun ta ruwaito.

Hukumomin tsaro sun ƙara tsaurara matakan tsaro a sansanonin NYSC, makarantu da guraren ibada bayan samun rahoton sirri

Hukumomin tsaro sun ƙara tsaurara sa ido a makarantu, sansanonin horas da matasa na NYSC, wuraren ibada da sauran wuraren da ake ganin suna cikin haɗari, bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa ’yan ta’adda na shirin kai hare-hare cikin haɗin gwiwa a sassa daban-daban na ƙasar. Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta bayar da wani gargaɗin tsaro da aka yaɗa zuwa sassa daban-daban na rundunar a faɗin ƙasar, inda ta yi gargadin yiwuwar hare-haren da aka shirya kaiwa da ka iya zo daidai da komawar ɗalibai makarantu a zangon karatu na shekarar 2026/2027. A cewar sanarwar ’yan sandan, bayanan sirrin da

Rundunar ‘yansandan ta kasa reshen Jihar Zamfara ta ce ta fara bincike domin gano wasu malaman Addinin Musulunci shida da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara a Zamfara.

Rundunar ‘yansandan ta kasa reshen Jihar Zamfara ta ce ta fara bincike domin gano wasu malaman Addinin Musulunci shida da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara a Zamfara. Rahotanni dai sun ce malaman suna hanyarsu ta komawa gida bayan zuwa wani taron addu’a na Jam’iyyar APC a Zamfara. ‘Yansandan sun ce tuni suka baza jami’ansu domin ceto malaman da aka sace. ’Yan bindiga sun sace limaman Musulunci shida a kan hanyar Dakko–Damri da ke ƙaramar hukumar Bakura ta Jihar Zamfara. Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar jiya Asabar, lokaci

Yan sanda sun kama Matar da ta yada cewa Opay zai daina aiki a ranar 31 ga watan Augusta

Rundunar ‘yansandan Najeriya ta kama Hafsat Abubakar, mai shekara 27, bisa zargin ƙirƙira da yaɗa wata takardar bogi da ke cewa kamfanin OPay zai daina aiki. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Anietie Iniedu, ya bayyana cewa an kama Hafsat ne ranar 4 ga Satumba 2026, bayan OPay ta kai ƙorafi ga rundunar ‘yansanda a ranar 31 ga Agusta. Ya ce cibiyar yaƙi da laifukan yanar gizo ta ‘yansanda ta gudanar da binciken ƙwaƙƙwafi na Internet, inda aka gano cewa takardar ta samo asali ne daga wani shafin X da Hafsat Abubakar ke amfani da shi. ‘Yansandan sun ce takardar ta bogi ce kuma an gabatar da it