Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce a halin yanzu babu wata tattaunawa da ke gudana tsakanin gwamnatinsa da Iran, duk da cewa yana sa ran za a cimma matsaya kan rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu nan ba da jimawa ba.

Da aka tambaye shi ko ya janye daga tattaunawar da ake yi da Tehran, Trump ya ce: “Ba ma tattaunawa da Iran a yanzu, amma za mu kai ga matsaya kan wannan batu. Hakan zai faru nan ba da jimawa ba.”

Trump ya ƙara da cewa mutane da dama na ganin cewa za a iya samun ci gaba kan batun ne bayan zaɓen tsakiyar wa'adin mulkin Amurka da ake sa ran gudanarwa.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta yi “abin da ya dace” wajen tunkarar Iran, yana mai bayyana takun saƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu a matsayin “ƙaramin rikici.”

Kalaman shugaban na Amurka na zuwa ne a daidai lokacin da babban kwamandan sojin Pakistan, Field Marshal Asim Munir, ya kai ziyara Tehran. Ana kallon Pakistan a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da suka taka rawa wajen ƙoƙarin sasanta rikicin tsakanin Washington da Tehran.

Haka kuma, kafin ziyarar Munir, Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya ziyarci Iran domin tattaunawa da jami'an ƙasar kan batutuwan da suka shafi dangantakar ƙasashen biyu da yanayin siyasar yankin.

Ziyarorin jami'an Pakistan da Rasha na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da sa ido kan yiwuwar sake buɗe tattaunawa tsakanin Amurka da Iran, da kuma ƙoƙarin da ake yi na samar da mafita ga takun saƙar da ke tsakaninsu.