Kwamandan NDLEA na Jihar Jigawa, Hassan Katangana K, ya yi kira ga matasa da su guji shiga dabar siyasa, yana mai gargaɗin cewa irin waɗannan ayyuka na iya jefa rayuwarsu da makomarsu cikin haɗari.

Ya kuma buƙaci iyaye da su ƙara sanya ido kan ’ya’yansu, tare da ba su tarbiyya mai kyau domin kare su daga shaye-shaye da sauran halayen da za su iya lalata makomarsu.

A yayin tattakin, Mataimakiyar Kwamandan Sashen Ba da Shawara, Jinya da Gyaran Hali ta NDLEA, Fatima Muhammad Dibal, ta bayyana irin ayyukan da hukumar ke gudanarwa a Jihar Jigawa wajen ba da shawarwari, kulawa da taimaka wa mutanen da ke fama da matsalolin amfani da miyagun ƙwayoyi.

Ta jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a da kuma samar da tallafi ga masu fama da matsalar shaye-shaye domin taimaka musu su samu sauƙi da komawa rayuwa mai inganci.

Haɗin gwiwar NDLEA da NUJ na daga cikin ƙoƙarin wayar da kan al’umma, musamman matasa, game da illolin shaye-shaye da kuma buƙatar kauce wa shiga rikice-rikicen siyasa.

An yi kira ga iyaye, malamai, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa kai wajen kare matasa daga shaye-shaye da daba ta siyasa, domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar.