Lamarin ya jawo hankalin jama’a bayan bayyanar wani bidiyo da ke nuna iyalan cikin mawuyacin hali a hannun masu garkuwa da mutane. Bidiyon ya haifar da kakkausar suka daga ’yan Najeriya, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ya yi kira da a gaggauta ceto iyalan.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kaduna, Ahmed Maiyaki, ya bayyana cewa gwamnatin jihar tana sane da halin da waɗanda aka sace suke ciki, kuma tana ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da kuɓutarsu.
Maiyaki ya ce, bisa umarnin gwamnan jihar, ana ci gaba da tattaunawa da jami’an tsaro domin ceto iyalan, tare da ƙarfafa matakan tsaro don kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta samu labarin lamarin tun kafin bidiyon ya bazu, kuma tun a lokacin aka fara ɗaukar matakan da suka dace domin ganin an kuɓutar da waɗanda aka sace.
Tun da farko, rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta bayyana cewa ta kama wasu mutane da ake zargi da hannu ko alaƙa da sace iyalan. Har yanzu, babban abin da ake jira shi ne tabbatar da kuɓutar da magidancin, matarsa da jaririyarsu cikin aminci.
