Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta gargaɗi kwamandojin ta a faɗin ƙasar da su kasance cikin shiri, sakamakon bayanan sirri da ke nuna yiwuwar kai hare-haren ta’addanci a makarantu, wuraren ibada, sansanonin NYSC da sauran wuraren da ake ganin suna cikin haɗari.
A cikin wata sanarwa da Sashen Ayyuka na rundunar ya fitar, an ce ana sa ran yiwuwar hare-haren ne a daidai lokacin da ake shirin fara sabon zangon karatu na shekarar 2026/2027.
Rundunar ta umarci kwamishinonin ’yan sanda da sauran jami’an tsaro da su ƙara sintiri, binciken ababen hawa da mutane, tare da ƙarfafa matakan tsaro a wuraren da ake ganin za su iya fuskantar barazana.
Jami’an tsaro sun ce akwai zargin wasu ’yan bindiga na yin zirga-zirga ta hanyar Katsina da Kaduna zuwa Jihar Filato. Haka kuma, ana zargin wasu da ake dangantawa da mayaƙan ISWAP da abokan hulɗarsu na cikin gida da gudanar da bincike kan wasu wuraren da ake zargin suna shirin kai wa hari.
Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta ce tana sa ido kan lamarin, yayin da Hukumar Tsaron Fararen Hula da Kare Al’umma, NSCDC, ta ce ta ƙarfafa tsarin tattara bayanan sirri tare da tura jami’ai na musamman domin ƙara kare makarantu.
Masana tsaro sun yi kira ga jama’a da su kasance masu sa ido tare da kai rahoton duk wani mutum, abin hawa ko wani yunƙuri da suka yi zargin ba shi da tushe ga hukumomin tsaro.
Sun kuma jaddada buƙatar ƙarfafa tattara bayanan sirri da ɗaukar matakan kariya tun kafin hare-hare su faru, musamman yayin da Nijeriya ke tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
A nasa ɓangaren, Ƙungiyar Iyaye da Malamai ta Nijeriya ta yi kira da a ƙara tsaurara matakan tsaro a makarantu, tare da amfani da fasahar zamani wajen gano abubuwan da ake zargi. Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnati ta farfaɗo da shirin Safe School Initiative , wato Shirin Kare Makarantu.
Duk da wannan gargaɗi, jami’an tsaro sun buƙaci iyaye da kada tsoro ya hana su barin ’ya’yansu su koma makaranta, suna jaddada cewa kare makarantu nauyi ne da ya rataya kan jami’an tsaro, makarantu, iyaye da al’umma bakiɗaya.
