Wata babbar kotun jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya ta yanke wa wani mutum mai suna Abubakar Musa, wanda aka fi sani da Daddy, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same shi da laifin kashe matarsa.
Rahoton gidan talabijin na Najeriya (NTA) ya bayyana cewa kotun, mai zama a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, ta samu Musa mai shekaru 45 da laifin kashe matarsa mai suna Ammi Mamman a shekarar 2024.
A ranar 4 ga watan Janairun 2024 ne rundunar 'yan sandan jihar Yobe ta kama mutumin bisa zargin kashe matarsa a rukunin gidajen New Bra-Bra Housing Estate da ke Damaturu, kafin daga bisani ta gurfanar da shi a gaban kotu.
Bayan shari'ar da ta ɗauki kusan shekaru biyu, alƙalin Babbar Kotun Jihar Yobe ta 1 ya yi watsi da ikirarin wanda ake tuhuma na cewa ba shi da laifi.
Alƙalin ya bayyana cewa hujjojin da aka gabatar a gaban kotun ba su goyi bayan ikirarin nasa ba, yana mai cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da tuhumar kisan kai ba tare da barin wata tantama mai ma'ana ba.
Bisa hukuncin da kotun ta yanke, an ɗora wa Abubakar Musa hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon samunsa da laifin kisan kai.
Sai dai rahoton NTA ya bayyana cewa wanda aka yanke wa hukuncin yana da damar ɗaukaka ƙara cikin wa'adin da doka ta tanada. Idan bai ɗaukaka ƙara ba, za a iya aiwatar da hukuncin bisa tanade-tanaden doka.
