Gwamnan jihar ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai wa iyalan a gidan kulawa na gwamnatin jihar, inda suka ci gaba da samun kulawar lafiya bayan an sallame su daga asibiti.

Gwamnan ya bayyana gamsuwarsa da yadda lafiyar iyalan ke ƙara inganta, yana mai cewa gwamnati za ta tabbatar sun samu kulawar da ta dace har zuwa lokacin da za su murmure sarai.

Ya ce abin da ya faru da iyalan na nuna irin raɗaɗin da matsalar rashin tsaro ke jefa al’umma a ciki, yana mai jaddada cewa kare rayukan jama’a da tabbatar da zaman lafiya na daga cikin muhimman nauyin da ke wuyan gwamnati.

A cewarsa, tallafin da za a ba iyalan ba zai tsaya ga samar musu da matsuguni da biyan kuɗin magani kaɗai ba, domin gwamnati za ta tabbatar sun samu kulawar ƙwararru kan lafiyar kwakwalwa da walwala, domin taimaka musu wajen farfaɗowa da sake gina rayuwarsu.

Gwamnan ya ƙara da cewa dawowar iyalan cikin ’yanci ta ƙara wa gwamnati ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da yaƙi da ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka. Ya ce za a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro tare da kusantar al’ummomi domin inganta tsaro a faɗin jihar.

Haka kuma, ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa nuna damuwa da bibiyar lamarin, tare da yabawa Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, da sauran hukumomin tsaro bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da dawowar iyalan cikin aminci.

A nasa ɓangaren, Malam Ahmed Abubakar Zakka ya gode wa Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jihar Kaduna da jami’an tsaro bisa ƙoƙarinsu da kulawar da suka nuna masa da iyalinsa a lokacin da suke cikin wannan mawuyacin hali.

Zakka ya bayyana jin daɗinsa kan kulawar da ake ba shi, yana mai cewa yana da ƙwarin gwiwar cewa lafiyarsa za ta ci gaba da inganta har zuwa lokacin da zai samu cikakkiyar murmurewa.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta jaddada cewa lafiyar iyalan da kuma tabbatar da cikakkiyar farfaɗowarsu za su ci gaba da kasancewa cikin abubuwan da za ta bai wa fifiko a watanni masu zuwa.