Jordan da Iraq sun haramta amfani da manhajar Telegram
Kasashen Jordan da Iraq sun sanar da haramta amfani da manhajar sada zumunta ta Telegram, bisa dalilan tsaron ƙasa.
Ammasco Radio90.7 FM · Gaskiya Tushen NasaraAMMASCO RADIO NEWSROOM
Kasashen Jordan da Iraq sun sanar da haramta amfani da manhajar sada zumunta ta Telegram, bisa dalilan tsaron ƙasa.
Rahotanni daga ƙasar Bahrain sun ce an yanke wa Musulmai ’yan Shi’a sama da 60 hukuncin ɗaurin rai da rai bisa zargin aikata laifukan ta’addanci da ake dangantawa da ƙasar Iran.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bai wa kowace ‘yar wasan tawagar Flamingos ta Najeriya kyautar naira miliyan 10, biyo bayan nasarar da suka samu a gasar cin kofin duniya ta mata ‘yan ƙasa da shekaru 17.
Kamfanin Rukunin Kasuwar Hannun Jari ta Najeriya, NGX Group, ya sanar da sayen kashi 10 cikin 100 na hannun jarin Kasuwar Hannun Jari ta Nairobi da ke ƙasar Kenya.
Ghana na shigo da tan 42 da rabi zuwa tan 62 na sinadarin mercury a duk shekara ta hanyoyin da ba su dace ba, inda ake amfani da shi wajen haƙar ma’adinai, musamman a ƙananan wuraren haƙar zinare.
Majalisar yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC ta sanar da wani sabon shirin tsaro na shekaru biyar ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da nufin magance matsalar rashin tsaro da ta daɗe tana addabar Najeriya.
Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Rotimi Amaechi, ya zargi hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC, da shirin kama shi gabanin babban zaɓen ƙasar.
Sakataren harkokin sufuri na Amurka ya buƙaci Majalisar Dokokin ƙasar da ta amince da ware ƙarin kuɗaɗe domin inganta tsarin zirga-zirgar jiragen sama, bayan da aka samu tangarɗa da ta haddasa dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na tsawon lokaci.
Hukumar kula da bayanan sirri ta ƙasar Italiya ta ci kamfanin Meta, mai mallakar Facebook, tarar Yuro miliyan 805, kwatankwacin fam miliyan 670 ko dala miliyan 887, bisa zargin amfani da hotuna da bidiyon masu amfani da wayoyin Android ba tare da samun takamaiman izininsu ba.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa al’ummar jihar Filato cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙarin sake gina al’ummomin da hare-haren ’yan ta’adda suka shafa, tare da mayar da mutanen da suka rasa matsugunansu zuwa garuruwansu na asali.
Wani kazamin faɗa tsakanin ƙungiyoyin ƴanbindiga da kuma ƴan banga ya janyo mutuwar sama da mutum 50 a jihar Zamfara, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Gwamnatin jihar Bauchi ta dakatar da Sarkin Lame, Alhaji Yakubu Aliyu, sakamakon zargin karɓar haraji ba bisa ƙa’ida ba, da kuma tsoma baki a harkokin filaye da haƙar ma’adanai.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga ’yan siyasa da magoya bayansu da su guji tayar da rikici yayin gudanar da yaƙin neman zaɓe gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Kamfanin Microsoft ya nemi afuwa kan katsewar wasu daga cikin ayyukansa da manhajojinsa a sassa daban-daban na duniya.
Kamfanin fasahar sadarwa na Microsoft da ke Amurka ya sanar da fuskantar matsala a wasu daga cikin ayyukansa na intanet, lamarin da ya shafi manhajojin aika saƙonnin imel na Outlook da kuma dandamalin sadarwa na Teams a sassa daban-daban na duniya.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya ranar 28 ga Nuwamba, 2026, domin gudanar da gwajin tantance masu zaɓe da kaɗa ƙuri'a a faɗin Nijeriya, a wani mataki na shirye-shiryen babban zaɓen ƙasar na shekarar 2027.
Gwamnatin Jihar Sokoto ta ware kuɗi har naira biliyan 5.5 domin gyara da dawo da wutar lantarki a ƙananan hukumomin Binji, Tangaza, Gudu da Silame, waɗanda suka shafe kusan shekaru 10 ba tare da samun wutar lantarki ba.
Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ta sake bayyana damuwarta kan cibiyar sarrafa sinadarin Uranium ta Iran da ke birnin Isfahan.
Ƙungiyar Masu Gidajen Burodi ta Najeriya (PBAN) ta bayyana cewa sama da kashi 40 cikin 100 na mambobinta sun daina gudanar da sana'ar saboda tsadar kayayyaki da hauhawar kuɗin gudanar da kasuwanci.
Kamfanin Nvidia ya naɗa babbar jami’ar harkokin kuɗinsa, Colete Kress, a matsayin shugabar riƙon ƙwarya, yayin da majalisar gudanarwar kamfanin ke neman wanda zai maye gurbin babban jami’in gudanarwarsa, Jensen Huang.