Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya yi bayani kan yadda aka kashe Naira biliyan 10 da aka amince da warewa a watan Yuni domin shirye-shiryen tunkarar cutar Ebola.
Atiku ya yi wannan kira ne a cikin wata sanarwa da daraktan sadarwa da dabarun siyasarsa, Phrank Shaibu, ya fitar da yammacin Laraba.
Kiran nasa ya biyo bayan sanarwar Ministan Lafiya na Najeriya, Ali Pate, kan bullar cutar Ebola a Abuja, da kuma gano mutane 44 da suka yi mu'amala da matar da ake zargin ta shigo da cutar daga Uganda.
Atiku ya ce bullar cutar ta haifar da tambayoyi kan irin shirye-shiryen da gwamnati ta yi da kuma yadda hukumomin lafiya suka mayar da martani kan lamarin.
Ya jaddada cewa ya kamata gwamnati ta nuna gaskiya wajen bayyana yadda aka kashe kuɗaɗen da aka ware domin tunkarar cutar, yana mai cewa 'yan Najeriya sun cancanci samun bayanai kan matakan da ake ɗauka domin kare lafiyarsu.
A cikin sanarwar, Atiku ya ce: “Ebola babbar barazana ce ga lafiyar jama'a. 'Yan Najeriya sun cancanci ɗaukar mataki cikin gaggawa, jagoranci mai inganci da gaskiya.”
Ya kuma buƙaci Tinubu ya yi cikakken bayani kan yadda aka kashe Naira biliyan 10 da aka ware a watan Yuni domin shirin tunkarar cutar Ebola.
Atiku ya tambayi dalilin jinkirin tabbatar da bullar cutar
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi tambayoyi kan jadawalin shigowar majinyaciyar da ake zargin ta shigo da cutar, lokacin da ta fara nuna alamomi da kuma lokacin da hukumomi suka tabbatar da bullar cutar.
A cewarsa, majinyaciyar ta isa Najeriya a ranar 5 ga watan Oktoba, ta fara nuna alamomin cutar a ranar 7 ga watan Oktoba, sannan ta nemi kulawar likita a wani asibiti mai zaman kansa a ranar 11 ga watan Oktoba.
Atiku ya ce gwamnati ba ta tabbatar da bullar cutar ba sai ranar 20 ga watan Oktoba, kwanaki tara bayan majinyaciyar ta nemi kulawar likita a asibitin.
Ya bayyana damuwa kan wannan tazara ta lokaci, yana mai cewa lamarin ya kamata ya sa a binciki yadda tsarin sa ido, gano cututtuka da sanar da jama'a ke aiki.
Sai dai ya zuwa lokacin fitar da wannan rahoto, ba a gabatar da cikakken bayani kan yadda aka kashe kuɗaɗen da aka ware ko kuma martanin gwamnatin tarayya ga tambayoyin Atiku ba
