An sauke Limamin Masallacin Unguwar Madina da ke cikin garin Bauchi, Dahiru Abubakar, daga muƙaminsa bayan zargin yaɗa manufofin sake zaɓen Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a cikin wa'azinsa.
Rahoton jaridar Daily Trust ya bayyana cewa limamin ya kasance yana amfani da lokutan wa'azi bayan kammala sallolin farilla wajen bayyana ra'ayoyin da ake kallon suna goyon bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu a shekarar 2027.
Da yake magana kan lamarin, Dahiru Abubakar ya ce wa'azinsa na mayar da hankali ne kan jan hankalin al'umma su guji ɗora wa Shugaba Tinubu alhakin matsalolin tattalin arziki da tsaro da ƙasar ke fuskanta. Ya danganta waɗannan ƙalubale da abin da ya kira alamomin ƙarshen zamani.
Ya ce: “Na kasance ina wa'azin mutane su daina ɗora alhakin matsalolin tsaro da ƙalubalen tattalin arziki a kan Shugaba Tinubu. Ina kuma ƙarfafa musu gwiwa su sake zaɓensa tare da ba shi wata dama a zaɓen 2027 domin ya ci gaba da manufofinsa.”
Limamin ya ƙara da cewa wa'azinsa ya fi mayar da hankali kan tsoron Allah da kyautata ayyukan yau da kullum, yana mai cewa Allah ne kaɗai zai iya kawo ƙarshen matsalolin tsaro ta hanyar amsa addu'o'in bayinsa.
Ya kuma ce yana amfani da misalan matsalolin tsaro da ke faruwa a wasu ƙasashen Afirka, ciki har da Sudan, Chadi da Mali, wajen bayyana cewa matsalolin tsaro ba su taƙaita ga Najeriya kaɗai ba.
A nasa ɓangaren, shugaban kwamitin gudanarwar masallacin, Imam Abubakar Jibrin, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce matsalar da kwamitin ke da ita da limamin ba ta tsaya kan zargin goyon bayan Tinubu kaɗai ba.
A cewarsa, kwamitin ya nuna damuwa kan yadda limamin ke tara mutane a gaban masallacin, da kuma shiga cikin masallacin da gangan domin tattauna harkokin siyasa.
Ya ce waɗannan abubuwa na daga cikin dalilan da suka jawo rashin jituwar da ta kai ga sauke limamin daga muƙaminsa.
