Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM) ta yi gargaɗin cewa kusan mutum 874,000 na iya rasa matsugunansu a Somalia cikin watanni uku masu zuwa sakamakon barazanar ambaliyar ruwa.
Hukumar ta bayyana cewa cikar koguna da mamakon ruwan sama na barazana ga al'ummomin da tuni suke fama da matsalolin fari da yawan ƙaura daga muhallansu.
Shugaban IOM a Somalia, Manuel Marques Pereira, ya ce akwai fargabar cewa dubban iyalai za su rasa gidajensu na tsawon makonni sakamakon ambaliyar.
Ya bayyana cewa mutane da dama sun riga sun bar muhallansu, kuma ba su da isassun hanyoyin da za su dogara da su wajen tunkarar sabon bala'in.
Pereira ya yi kira da a samar da kuɗaɗen agajin gaggawa domin taimaka wa al'ummomin da ke cikin haɗari su kare rayukansu da gidajensu.
Sabbin hasashen da IOM da Hukumar 'Yan Gudun Hijira ta Denmark (DRC) suka fitar sun nuna cewa mutum 874,319 na iya barin gidajensu tsakanin Oktoba da Disamba. Hasashen ya nuna cewa ambaliya ce za ta haddasa kashi 92 cikin 100 na wannan ƙaura.
Gargaɗin na zuwa ne yayin da Somalia ke shiga lokacin damina, inda ake hasashen samun ruwan sama fiye da yadda aka saba sakamakon tasirin yanayin El Niño.
IOM ta kuma bayyana cewa zuwa yanzu, ta samu kashi 14.4 cikin 100 ne kawai na kuɗaɗen da take buƙata domin aiwatar da shirinta na tunkarar ambaliyar, lamarin da ke nuna gibin kuɗaɗen da ake buƙata don tallafa wa al'ummomin da ke cikin haɗari.
Tuni dai aka fara samun alamun ambaliya a wasu yankuna, ciki har da Doolow, Jowhar da Baidoa. Haka kuma, ana hasashen cewa Beledweyne da Gaalkacyo na daga cikin wuraren da za su fi fuskantar barazanar ambaliya da kuma tilasta wa jama'a barin gidajensu.
Hukumar ta jaddada muhimmancin samar da tallafin gaggawa domin rage illolin ambaliyar da kuma taimaka wa al'ummomin da ke fuskantar barazanar rasa matsugunansu.
