Gasar ta bana ta ƙunshi ƙungiyoyi takwas, waɗanda suka haɗa da wakilan jihohin Kano, Yobe, Sokoto, Kebbi da Nasarawa, da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja. Sauran ƙungiyoyin su ne Team Founder da Team President.

An raba ƙungiyoyin zuwa rukuni biyu, inda Kano Pillars Para Soccer take cikin Rukuni na A tare da Yobe, Sokoto da Team President.

A Rukuni na B kuwa, akwai Abuja, Kebbi, Nasarawa da Team Founder.

Kano Pillars Para Soccer za ta fara wasanta na farko ne da takwararta ta Jihar Yobe a yau Laraba, 21 ga Oktoba, 2026, inda take fatan samun nasara domin ƙarfafa burinta na lashe kofin gasar ta bana.

Da yake tsokaci kan shirye-shiryen ƙungiyar, mai horar da ‘yan wasan, Coach Ibrahim Musa, ya bayyana cewa ‘yan wasan sun kammala shirye-shiryensu kuma suna da cikakken shiri domin taka rawar gani a gasar.

Ya kuma yabawa Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, tare da Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Alhaji Muhammad Tukur Babangida, bisa ci gaba da goyon bayan da suke bai wa harkokin wasanni a jihar.

Kano Pillars Para Soccer na fatan wakiltar jihar cikin nasara, yayin da take fafatawa da sauran ƙungiyoyi domin lashe gasar ta bana.