Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya tsohon gwamnan jihar kuma Sanata, Rabiu Musa Kwankwaso, murnar cika shekara 70 da haihuwa, tare da yabawa da gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.
A cikin saƙon taya murnar, Gwamna Yusuf ya bayyana zagayowar ranar haihuwar Kwankwaso a matsayin wata muhimmiyar dama ta waiwayen rayuwarsa, jagorancinsa da kuma gudunmawar da ya bayar ga hidimar jama’a tsawon shekaru.
Gwamnan ya yaba da rawar da Kwankwaso ya taka wajen ci gaban siyasar Kano, yana mai cewa tsohon gwamnan ya bayar da gudunmawa a fannoni da dama, ciki har da shugabanci, samar da ababen more rayuwa da ƙarfafa dimokuraɗiyya.
Ya ce wannan rana ta musamman na ba da damar tunawa da ayyukan da Kwankwaso ya gudanar da kuma tasirinsu ga al’ummar Kano.
Dangantakar Siyasa Ta Yi Tsami Bayan Sauya Sheƙar Abba
Taya murnar na zuwa ne a daidai lokacin da dangantakar siyasa tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da jagoransa na siyasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ta shiga wani sabon yanayi bayan gwamnan ya fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
A ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026, Abba Kabir Yusuf ya sanar da ficewarsa daga NNPP, kafin daga bisani ya koma APC a hukumance a ranar Litinin, 26 ga Janairu, 2026.
Matakin ya jawo sauye-sauye a dangantakar siyasa tsakanin tsoffin abokan tafiyar, waɗanda suka yi aiki tare a ƙarƙashin tsarin siyasar Kwankwasiyya.
A lokacin da yake bayyana dalilin sauya shekar, Gwamna Yusuf ya ce ya ɗauki matakin ne bisa la’akari da yanayin siyasar Najeriya da kuma buƙatar bin hanyar da zai taimaka wajen kawo ci gaba ga al’ummar Jihar Kano.
Kwankwaso Ya Ce Abba da Muƙarrabansa Za Su Yi Nadama
A wata hira da BBC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf da wasu daga cikin muƙarrabansa za su yi nadamar raba gari da tsarin siyasar da suka daɗe suna tafiya tare.
Sai dai saƙon taya murnar cika shekara 70 da haihuwa da Gwamna Yusuf ya aika ya nuna cewa har yanzu ana iya bayyana girmamawa ga gudunmawar tsohon gwamnan, duk da bambance-bambancen siyasa da suka shiga tsakaninsu.
Zagayowar ranar haihuwar Kwankwaso ta sake jawo hankali kan tarihin jagorancinsa a Kano da kuma rawar da ya taka a siyasar Najeriya.
