Tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi ya bayyana haka ne a daidai lokacin da jam'iyyar ke shirin fidda ɗan takarar da zai tsayawa ADC a matsayin mai neman kujerar shugabancin Najeriya a zaɓe mai zuwa.


Bisa tsarin karɓa karɓa da ake, shugabancin Najeriyar zai tsaya ne a kudu har zuwa shekarar 2031.


Amaechi na daga cikin masu sha'awar takarar shugabancin jam'iyyar la'akari da cewar ya sayi fom tare da Atiku Abubakar da Mohammed Hayatuddeen.