Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga likitocin Najeriya da sauran ƙwararrun ma’aikatan lafiya da ke aiki a ƙasashen waje da su dawo gida domin ba da gudunmawarsu wajen bunƙasa harkokin kiwon lafiya a ƙasar.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar Ƙungiyar Likitocin Najeriya da ke Ƙasashen Waje, tare da Shugabar Hukumar ‘Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, a Abuja.
Ya ce Najeriya na buƙatar ilimi, ƙwarewa da gogewar ‘ya’yanta da suka yi fice a ƙasashen waje domin gina ingantaccen tsarin kiwon lafiya da zai samar da ingantacciyar kulawa ga al’umma.
Shugaban ya yabawa likitocin bisa ayyukan jin ƙai da suka gudanar a sassa daban-daban na ƙasar, inda suka bayar da tallafin jinya, gudanar da tiyata, ba da shawarwari kan kiwon lafiya da kuma wasu ayyukan ceton rayuka.
Haka kuma, Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a fannin kiwon lafiya, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙwararrun ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje, domin rage ƙaurar ƙwararru da kuma inganta tsarin kiwon lafiya a faɗin ƙasar.