Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya Akanta Janar na Tarayya, Dakta Shamseldeen Babatunde Ogunjimi, murnar zaɓensa a matsayin Shugaban Ƙungiyar Akantoci Janar ta Afirka (African Association of Accountant-Generals – AAAG).

Ogunjimi ya samu nasarar ne bayan wata zaɓe mai cike da gasa da ya fafata da 'yan takara daga ƙasashen Tanzania da Gambiya, a yayin Babban Taron Shekara-shekara na ƙungiyar da aka gudanar kwanan nan a Masarautar Eswatini.

A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, an bayyana cewa zaɓen Ogunjimi ya zama shugaban ƙungiyar nahiyar wata babbar nasara ce ga Najeriya, kuma shaida ce ta ƙoƙarin da ƙasar ke yi wajen inganta gaskiya, riƙon amana da ƙwarewa a harkokin gudanar da kuɗaɗen gwamnati.

Shugaba Tinubu ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa, a ƙarƙashin jagorancin Ogunjimi, ƙungiyar za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afirka, da musayar ingantattun dabaru, da bunƙasa ƙwarewar hukumomi, tare da inganta sauye-sauyen da za su tabbatar da ingantaccen tsarin gudanar da kuɗaɗen gwamnati a faɗin nahiyar.

Shugaban ya kuma yi wa Dakta Ogunjimi fatan samun nasara a sabon muƙaminsa, tare da tabbatar masa da cikakken goyon bayan Gwamnatin Tarayya yayin da yake gudanar da wannan muhimmin nauyi na nahiyar Afirka.