Iran ta samu damar fitar da kusan gangar ɗanyen mai miliyan 73 cikin ƙasa da wata guda, bayan da Amurka ta ɗan sassauta wasu daga cikin takunkuman da ta ƙaƙaba mata kan fitar da man fetur.
Rahotanni sun nuna cewa daga ƙarshen watan Yuni zuwa tsakiyar watan Yuli, jiragen dakon mai na Iran da dama sun fara bayyana a yankin ruwan gabashin Malaysia, suna jigilar ɗanyen mai zuwa kasuwannin ƙasashen Asiya.
Kamfanin Kepler, mai sa ido kan harkokin jigilar makamashi, ya bayyana cewa darajar ɗanyen man da Iran ta fitar a wannan lokaci na iya kaiwa kusan dala biliyan shida.
Sai dai duk da wannan ci gaba, rahotanni sun nuna cewa wasu manyan kamfanonin kasar China, waɗanda ke daga cikin manyan masu sayen man Iran, sun rage yawan sayayyar da suke yi.
A wani ɓangaren kuma, Amurka ta sake janye sassaucin takunkuman da ta bai wa Iran a ranar 7 ga Yuli, bayan ta amince na ɗan lokaci da sayar da ɗanyen man ƙasar tun daga 21 ga Yuni.