Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Janar Abdulrahman Dambazau mai ritaya, ya bayyana cewa kafa ‘yan sandan jihohi zai yi tasiri ne kawai idan an gina tsarin su bisa ƙwarewa da bin ƙa’ida.
Dambazau ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), inda ya ce bai kamata gwamnoni su mallaki ikon sarrafa ‘yan sandan jihohi ba, yana mai cewa hakan na iya sanyawa a yi amfani da su wajen danniya ko yaƙar abokan hamayyar siyasa.
Ya kuma jaddada muhimmancin tantance jami’ai yadda ya kamata, horas da su tare da samar musu da kayan aiki da walwala domin tabbatar da ingantaccen aiki da hana cin zarafi.
A cewarsa, dole ne a samar da tsarin sa ido na ƙasa baki ɗaya tare da ƙa’idojin aiki domin kauce wa take haƙƙin ɗan Adam ko rikidewar rundunar zuwa ƙungiyoyin ƙabilanci.