Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan yadda matsalar tsaro ke ƙara muni a ƙasar nan, yana mai cewa yawaitar kashe-kashe da garkuwa da mutane alama ce ta gazawar shugabanci.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya nuna damuwa matuƙa kan sace ɗalibai da malamai a Ogbomoso da kuma kashe wasu mutane a Jihar Katsina, ciki har da wata mata mai juna biyu.
Ya ce abin takaici ne yadda gwamnati ke ci gaba da mayar da martani da fitar da sanarwar ta’aziyya bayan aukuwar hare-hare, maimakon ɗaukar matakan da za su hana faruwar irin waɗannan abubuwa.
Atiku ya bayyana cewa ’yan Najeriya sun gaji da jin irin kalaman cewa masu aikata laifuka za su fuskanci hukunci, alhali hare-haren na ci gaba da faruwa ba tare da an kawo ƙarshensu ba.