Gwamnatin ƙasar Togo ta sanar da cire buƙatar biza ga dukkan ‘yan ƙasashen Afirka da ke shiga ƙasar domin zama na wani ɗan lokaci.


Cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Tsaro ta Togo ta fitar a shafinta na X yau Talata, gwamnati tace duk wani ɗan Afirka mai riƙe da ingantaccen fasfo na ƙasarsa zai iya shiga Togo ba tare da neman biza ba domin zama har na tsawon kwanaki 30.


Gwamnatin Togo ta ce wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙara ƙarfafa haɗin kan ƙasashen Afirka tare da sauƙaƙa zirga-zirga tsakanin al’ummar nahiyar.


Sanarwar ta bayyana cewa shugaban majalisar ƙasar ya sake jaddada aniyarsa ta mayar da Togo cibiyar hulɗa da jama’a , haɗin kai da damar kasuwanci a tsakiyar nahiyar Afirka.

Sai dai duk da cire bukatar biza, gwamnatin ta ce matafiya za su ci gaba da cike takardar bayanan tafiya a shafukan gwamnati kafin akalla sa’o’i 24 da isa ƙasar domin samun takardar izinin shiga.