Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da samar da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana guda 166 domin rage matsalar karancin ruwa da fadada samar da tsaftataccen ruwa ga al’ummar jihar.


Mukaddashin Kwamishinan Albarkatun Ruwa na jihar, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce shirin wani bangare ne na matakan gaggawa da gwamnatin jihar ke dauka domin magance matsalar ruwa a yankuna daban-daban.


A cewarsa, ana sa ran rijiyoyin za su samar da kimanin lita miliyan 4.15 na ruwa a kullum tare da anfani ga mutane kusan 830,000 a yankunan da ke fama da karancin ruwa. Ya ce kowace rijiyar za ta rika samar da lita 25,000 na ruwa a rana tare da anfani ga mutum kusan 5,000.


Dakta Hashim ya bayyana cewa wannan shi ne kashi na farko na aikin, yana mai cewa gwamnati na shirin kara amincewa da wasu rijiyoyin a a fadin jihar Kano.