Chad ta ayyana dokar ta ɓaci a yankin Lake Chad kwanaki kaɗan bayan da mayakan Boko Haram suka kashe jami’an soji aƙalla 24 a wani sansanin soji da ke Barka Tolorom.

Dokar ta ɓacin za ta fara aiki daga daren 7 zuwa daren 27 ga watan Mayun 2026. Hukumomi sun bayyana cewa za a rufe iyakokin yankin tare da sanya dokar hana zirga-zirga domin ƙarfafa matakan tsaro.

A wata sanarwa da ya gabatar ta gidan talabijin na ƙasar, mai magana da yawun gwamnatin Chadi, Gassim Cherif, ya ce ɗaukar matakin zai taimaka wajen kamo waɗanda ake zargi da kai harin, tare da dakile zirga-zirgar mutane, motoci da mashina a yankin.

Yankin Tafkin Chadi, wanda ya haɗa iyakokin Cameroon da Niger da Nigeria da kuma Chad, ya daɗe yana fama da hare-haren mayakan Boko Haram, musamman a ‘yan kwanakin nan da hare-haren suka ƙaru.