Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya umarci jami'an tsaro da su murkushe ƴan daba dake addabar cikin birnin Kano tare da magance ƴan fashin daji dake shigowa jihar ta kan iyakokin Katsina.
Kwamishinan ƴansandan Kano, CP Ibrahim Bakori ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron gaggawa na majalisar tsaron jihar Kano.
Kwamishinan ƴansandan ya ce al'ummar Kano za su fara ganin sauyi nan da kwanaki uku game da matsalar tsaron dake addabar jihar.