Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce ta tarwatsa wata ƙungiyar masu safarar mutane da ake zargin tana gudanar da ayyukanta a Abuja da wasu yankuna maƙwabta.

Jami’an tsaron sun kuma kuɓutar da mutum 30 ‘yan asalin Mali da ake zargin an tsare su a Nasarawa.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Anthony Placid ya fitar, ya ce jami’ai sun gano ayyukan ƙungiyar ne a wasu gidaje da ke yankunan Mararraba da Karu, inda ake zargin an killace mutanen.

‘Yan sanda sun ce sun kama mutum 13 da ake zargi suna da hannu a safarar mutanen.

A cewar rundunar, binciken ya fara ne bayan samun bayanan sirri kan ɓacewar wasu baƙi a Najeriya.

Binciken farko ya nuna cewa ƙungiyar na yaudarar matasa daga ƙasashe kamar Mali da Gabon, inda ake yi musu alƙawarin samar da ayyukan yi a Najeriya da kuma damar tsallakawa zuwa Turai.