Ɓarkewar cutar Ebola mai saurin yaɗuwa ta kashe aƙalla mutane 131 a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, kamar yadda jami’an ƙasar ta tsakiyar Afirka suka bayyana bayan sabunta adadin daga mutum 118 da aka sanar a baya. Likitoci na ci gaba da bibiyar sama da mutum 500 da ake zargin sun kamu da cutar.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) za ta gudanar da zaman kwamitin gaggawa a ranar Talata domin tattauna yadda cutar ke ƙara yaɗuwa.

“An shirya zaman kwamitin gaggawa nan gaba a yau,” in ji wani mai magana da yawun WHO ga AFP, kwanaki biyu bayan shugaban hukumar lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya ayyana ɓarkewar cutar a matsayin babban barazana ga lafiyar al’umma a duniya.

Nau’in Ebola mai suna Bundibugyo — wanda ba kasafai ake samu ba — ya sa WHO ta ɗaga matakin gargaɗi kan annobar saboda hatsarin da take haifarwa ga lafiyar duniya.

Mafi yawan waɗanda suka kamu suna Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, yayin da cutar ta bazu zuwa Uganda, inda aka fara gano wannan nau’in tsakanin shekarun 2007 zuwa 2008.