Iyalan sun gudanar da zanga-zanga a hedikwatar DSS da ke Abuja, bayan an kai El-Rufai hannun hukumar. Matar sa ta biyu, Asia El-Rufai, ta ce iyalan na fuskantar barazana da tsangwama tun bayan kama shi.

Ta bayyana cewa wata kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin El-Rufai tare da umarnin a ci gaba da tsare shi a hannun hukumar ICPC, amma daga baya aka kai shi ofishin DSS duk da umarnin kotuna biyu da suka hana hakan.

Asia ta kuma ce an hana El-Rufai ganin likitocinsa duk da umarnin kotu da ya ba shi damar samun kulawar likita da lauya ba tare da takura ba.

Iyalan sun buƙaci a mayar da El-Rufai hannun ICPC kamar yadda kotu ta umarta, tare da kawo ƙarshen abin da suka kira tsangwama ga iyalan.