Al'ummar Garin Dangada da Kewaye dake karamar hukumar Bagwai suna neman agajin mahukunta dasu kawo musu dauki na batun Samar da tsaro da kuma basu damar aiki da Mahukunta a bangaran tsaron yankin.
Rahotanin sun bayyana cewa tun bayan samun Labarin matsalolin tsaro a yankin Gwarzo, Shanono, Tsanyawa da Kunchi ( Gari) Kungiyar ci gaban Garin Dangada su himmatu wajen ganin sun temaka da harkokin tsaro, wajen Daukar Matasa aikin sunturi domin yaki da batagari a yankin Bagwai, Amma Sai gashi ana zargin wasu mutane suna hana Ruwa gudu.
Lamarin da a halin yanzu Al'ummar Garin Dangada su an karar da Mahukunta da Wakilan su a Majalisar Tarayya da Sanatan su da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusif dasu kalli matsalolin da suke ciki,,, a sanarwa Matasa aikin yi, da Samar musu da wutar lantarki,, tunda dai suna da Kungiya wacce zata temaka a Yaki matsalar tsaro a Garin Dangada da Kewayen ta.