Hukumar yaki da rashawa ta ICPC, ta musanta zarge-zargen cewa ta hana iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El’rufai ganawa da iyalansa ya yin da yake tsaren a hannun hukumar.

Ta cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta bakin mataimakin shugaban sashin hulda da jama’a na hukumar John Odey, ta ce wadannan labarai da ake yadawa basu da tushe.

Ya ce ikirarin da matar tsohon gwamnan ta yi na cewa hukumar ta hanata ganawa da mai gidan nata, ba gaskiya bane, inda ya ce tazo ziyarar ne mintuna 30 bayan lokacin da aka ware domin bada dama a gana da wanda ake tsare da shi.

Hukumar ta ce ya kamata a sanar da al’umma gaskiya abunda ya faru, ba tare da an yi musu wasa da hankali, ko basu bayanai na karya ba, kuma hukumar na aikinta kamar yadda doka ta tanada ba tare da muzgunawa ba.