Bayan samun 'yan sa'o'i na nishi, tsohon Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya sake afkawa hannun jami'an tsaro na DSS, jim kaɗan bayan da kotu ta bayar da belinsa a kan kuɗi naira miliyan 100. Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, ta gindaya tsauraran sharaɗan beli da suka haɗa da neman ma'aikacin gwamnati na matakin Level 17 mai gida a Maitama ko Asokoro da zai tsaya masa, to sai dai jami'an DSS ba su ba shi damar cin moriyar wannan beli ba.
Wannan sabon kamun ya biyo bayan zargin El-Rufai da datsar wayar Mashawarcin Shugaban Ƙasa a kan Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, wadda tuhuma ce ta daban da wadda hukumar ICPC ke yi masa. Majiyoyi sun tabbatar da cewa tun da fari ma, jami'an na DSS sun yi dako a harabar hukumar ICPC tun ƙarfe 7:00 na safe domin aiwatar da wannan kamun.
A ɓangare guda, majiya daga hukumar ICPC ta bayyana cewa sabbin zargi da DSS ke yi wa tsohon gwamnan ba su shafe su ba. Kamfanin ya ƙara da cewa matakansu na gurfanar da shi a gaban shari'a zai ci gaba da tafiya kamar yadda aka tsara, ba tare da la'akari da tsarewar da DSS ta yi masa ba.