Mai magana da yawun rudunar sojin ta Najeriya Sama'ila Uba ya fitar a jiya Asabar, ya ce: "Mun samu nasarar kai wani tsararren hari da muka shirya ƙarƙashin shirinta na yaƙi da ta'adanci, wanda yayi sanadiyar kisan Abu-Bilal al-Minuki, wanda yana ɗaya daga cikin ƴan ta'addan da ake da su a duniya".
Ta ce an samu nasarar harin ne da taimakon haɗin-gwiwa da tallafin haɗin-gwiwar Amurka wajen musayar bayyana shirri. "Tare da Amurka mun yi nasarar rusa gungun muggan ƴan ta'adda da ke barazana ga rayukan ƴan Najeriya, da sauran ƙasashen da ke Afirka ta yamma", inji sanarwan.
Sai dai, rundunar sojin ta Najeriya ba ta sanar da inda aka kai harin ba.
Rudunar sojin ta Najeriya ta danganta Abu-Bilal al-Minuki da hannu a sace ɗaliban makarantar ƴam mata da ke Dapchi, 2018, inda aka sace ɗalibai 100 a makarantar kwanan ta na ƴanmata, da ke yankin Arewa-maso-Gabashin ƙasar, wanda hakan ya jefa damuwa a faɗin ƙasar.