Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma Sanatan mazabar Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari, ya bukaci al’ummar Arewa da su mara wa Bola Ahmed Tinubu baya domin sake zabensa a shekarar 2027.
yari ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da malaman addinin Musulunci a garin Talata-Mafara ranar Asabar, inda ya ce lokaci ya yi da Arewa maso Yamma za ta rama alherin goyon bayan da yankin Kudu maso Yamma ya bai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari tsakanin shekarun 2015 zuwa 2023.
A cewarsa, haɗin kan siyasar Arewa da Kudu maso Yamma na da muhimmanci wajen tabbatar da nasarar jam’iyya da kuma daidaiton siyasar Nijeriya.
Ya ce yankin Kudu maso Yamma ya tsaya tsayin daka wajen mara wa Buhari baya a wa’adinsa na biyu, don haka ya dace Arewa ta yi irin wannan goyon baya ga Tinubu.