Hukumar Dakile Yaɗuwar Cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta tsaurara sa ido kan cutar Ebola bayan sake ɓullar cutar a ƙasashen Kongo da Uganda.

Hukumar ta bayyana cewa ta ɗauki matakan shiri domin hana shigowar cutar cikin Nijeriya, ciki har da ƙarfafa bincike a filayen jiragen sama da sauran mashigai na ƙasa.

NCDC ta kuma buƙaci ‘yan ƙasa da su kiyaye tsafta, su riƙa wanke hannu akai-akai, tare da kai rahoton duk wani mutum da ke nuna alamun cutar domin dakile yaduwarta.

Hukumar ta ce tana aiki tare da hukumomin lafiya na duniya domin tabbatar da an dakile duk wata barazanar yaɗuwar Ebola a ƙasar.