Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya buƙaci al’ummar Musulmi da su fara duba watan Zul-Hajji, wanda shi ne watan Sallah babba, daga gobe Lahadi 17 ga watan Mayun 2026 daidai da 29 ga Zulƙida 1447 Hijiriyya.
Wata sanarwa da shugaban kwamitin bayar da shawara kan harkokin addinin musulunci na majalisar Sarkin Musulmi kuma Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, ya fitar, ta buƙaci duk wanda ya ga wata ya sanar da hakimi ko uban ƙasa na kusa da shi don sanar da Majalisar Sarkin Musulmi.