‎Hukumomin lafiya na Afirka sun tabbatar da ɓullar cutar Ebola a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo , lamarin da ya janyo mutuwar mutane da dama.


‎Cibiyar Kula da Cututtuka ta Afirka ta bayyana cewa an samu mutane 246 da ake zargin sun kamu da cutar, yayin da mutum 65 suka rasu, ciki har da mutum huɗu da gwaje-gwaje suka tabbatar sun kamu da Ebola.


‎Hukumar ta ce an tabbatar da ɓullar cutar ne a lardin Ituri da ke gabashin ƙasar, inda ake ci gaba da sa ido tare da shirya taron gaggawa da ƙasashen Uganda da Sudan ta Kudu domin ƙarfafa matakan sa ido da dakile yaduwar cutar a yankunan.


‎Cutar Ebola cuta ce mai saurin yaɗuwa wadda ake kamuwa da ita ta hanyar hulɗa kai tsaye da ruwan jikin wanda ya kamu da ita, kuma tana haddasa zubar jini da lalacewar sassan jiki.