Gwamnatin Jihar Zamfara ta hana rakiyar maniyyatan aikin Hajji zuwa filin jirgin sama na Gusau yayin fara jigilar su zuwa ƙasa mai tsarki.
Wannan na cikin sanarwar da Mai Taimaka wa Gwamnan Jihar Zamfara kan Kafafen Sadarwa na Zamani Mugira Yusuf ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa maniyyatan jihar za su fara tashi zuwa ƙasa mai tsarki yau Jumu’a ta filin jirgin sama na Gusau.
Sanarwar ta jaddada cewa, duk wanda ke da ɗan uwa ko aboki cikin maniyyatan to ya yi musu bankwana a sansanin Alhazai, domin an hana rakiyar su zuwa filin jirgin saman.Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an dauki matakin ne domin tabbatar da tsaro da kuma sauƙaƙa gudanar da jigilar maniyyatan zuwa aikin Hajjin bana.