Jam'iyar PDP tsagin Tanimu Turaki SAN ya soki hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya soke hukuncinta na baya wanda ya umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta yi wa jam'iyar NDC rajista a matsayin jam'iyyar siyasa.


A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na bangaren, Ini Ememobong, ya fitar a ranar Juma'a, ya ce suna jiran samun cikakken kwafin hukuncin kotun (Certified True Copy), amma sun bayyana damuwa cewa hukuncin na iya ƙara takaita damar dimokuraɗiyya a Najeriya.


A ranar Juma'a, Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja, Jihar Kogi, ta soke hukuncinta na baya wanda ya umarci INEC ta yi wa NDC rajista a matsayin jam'iyyar siyasa.


Mai shari'a Isah Dashen ya bayyana cewa Peace Movement Party, wadda ta yi ikirarin mallakar tambarin da aka dogara da shi wajen samun hukuncin farko, tana daga cikin muhimman ɓangarorin da ya kamata a shigar da su cikin shari'ar, kuma ya dace a ba ta damar gabatar da hujjojinta kafin kotu ta yanke hukunci.