Jam'iyyar NDC ta bayyana cewa za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ta yanke, wanda ya soke umarnin da ya bai wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) damar yi mata rajista a matsayin jam'iyyar siyasa.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Jam'iyyar na Ƙasa, Sanata Moses Cleopas Zuwoghe, ya fitar, NDC ta ce ba ta amince da hukuncin da kotun ta yanke ba, wanda ya biyo bayan ƙarar da wata ƙungiya mai suna Peace Movement Party (PMP) ta shigar.
Jam'iyyar ta yi zargin cewa PMP ba jam'iyya ce mai rijista ba, kuma ba ta cikin ƙungiyoyin da ke neman rajista a halin yanzu. Saboda haka, ta bayyana mamakinta kan yadda kotun ta amince da buƙatar PMP ta sake duba hukuncin da aka yanke tun da farko.
NDC ta tuna cewa tun a watan Disamban 2025, kotu ta yanke hukuncin da ya ba ta damar kafa jam'iyya tare da umartar INEC ta yi mata rajista, inda ta ce hukumar zaɓen ta aiwatar da wannan umarni.
Sanarwar ta ce tun bayan samun rajista, jam'iyyar ta gudanar da rajistar mambobi, ta shirya taruka daga matakin mazaɓa zuwa na ƙasa, ta kammala zaɓen fidda gwani, sannan ta shiga wasu zaɓukan cike gurbi da aka gudanar a jihohin Nasarawa da Enugu.
Sai dai jam'iyyar ta jaddada cewa sabon hukuncin kotun bai soke rijistar NDC kai tsaye ba, illa dai ya soke hukuncin da ya tilasta wa INEC yi mata rajista.
NDC ta ce ta umarci lauyoyinta da su garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ƙalubalantar hukuncin, tana mai bayyana kwarin gwiwar cewa za ta samu nasara a mataki na gaba.