Sabon tsarin Gasar Kofin Duniya da aka faɗaɗa zuwa tawaga 48 ya fara haifar da muhawara, yayin da ake ƙara nuna damuwa kan yadda ake tantance ƙasashen da za su tsallaka daga matakin rukuni zuwa zagaye na gaba.

Ɗaya daga cikin misalan da ke nuna hakan shi ne halin da Koriya ta Kudu ke ciki, bayan ta sha kashi da ci 1-0 a hannun Afirka ta Kudu, sakamakon da ya bai wa Bafana Bafana damar kaiwa zagayen gaba a karon farko a tarihinta.

Duk da rashin nasarar, Koriya ta Kudu har yanzu na da damar tsallakawa zuwa zagaye na 'yan 32 a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da suka zo na uku mafi ƙoƙarin tattara maki.

Da maki uku da kuma banbancin ƙwallaye na -1, ana ganin akwai yiwuwar hakan ya isa ya ba ta tikitin zuwa zagaye na gaba.

Sai dai da a ce ana amfani da tsohon tsarin gasar Kofin Duniya na 2022, inda ƙasashe biyu kacal daga kowanne rukuni ke tsallakawa, da tuni Koriya ta Kudu ta fice daga gasar.

Sabon tsarin ya tanadi damar ƙasashen da suka zo na uku mafi yawan maki su tsallaka, domin cika adadin ƙasashe 32 da za su fafata a zagaye na biyu.

Masana da masu bibiyar ƙwallon ƙafa na ganin cewa wannan tsari na iya haifar da yanayi inda wasu ƙasashe za su buga wasanninsu da nufin samun wani takamaiman sakamako da zai ba su damar tsallakawa, ko ma su kauce wa haɗuwa da wasu manyan abokan hamayya a zagaye na gaba.

Hakan ya sa ake ci gaba da tattaunawa kan ko sabon tsarin zai ƙara armashi ga gasar ko kuma zai haifar da wasu matsaloli ga adalci da gasa mai inganci.