Akalla mutum 17 ne suka jikkata bayan wata mota ta kutsa cikin taron jama'a a garin Cabo San Lucas na ƙasar Mexico, yayin da mutane ke murnar nasarar da tawagar ƙasar ta samu a Gasar Kofin Duniya.

A wata sanarwa da ƙaramar hukumar Los Cabos ta fitar, an bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Laraba a wani shahararren wurin yawon buɗe ido, lokacin da motar ta kutsa cikin taron mutane saboda wasu dalilai da har yanzu hukumomi ke bincike.

Sanarwar ta ce an ba mutane 17 kulawar gaggawa bayan faruwar lamarin, ciki har da direban motar, wanda tuni jami'an tsaro suka kama domin ci gaba da bincike.

A halin da ake ciki, wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna motar tana kutsa cikin taron jama'ar. Sai dai har yanzu ba a tabbatar da sahihancin bidiyon ba.

Cabo San Lucas, da ke jihar Baja California, na ɗaya daga cikin manyan wuraren yawon buɗe ido a Mexico, kuma yana cikin yankin Los Cabos, wanda ya haɗa da San José del Cabo da sauran wuraren shakatawa.

Lamarin ya faru ne bayan dubban magoya baya sun fito kan tituna domin murnar nasarar da Mexico ta samu da ci 3-0 a kan Jamhuriyar Czech a wasanta na ƙarshe a matakin rukuni na Gasar Kofin Duniya.

Hukumomi sun ce ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin aukuwar lamarin da kuma ɗaukar matakan da suka dace kan wanda ake zargi.