Yau juma’a ake cika shekaru 78 da fara mamayar da Isra’ila ke yiwa yankunan Falasɗinawa, ranar da ake yiwa laƙabi da Naƙba ko kuma ranar baƙin ciki ga yankin na Falasɗinu.
A ranar 15 ga watan Mayun shekarar 1948 ne, Isra’ilar ta fara mamaye yankunan Falasɗinawa tare da mayar da su mallakinta, inda a rana guda ta tayar da jumullar mutanen da yawansu ya kai dubu 700 zuwa miliyan guda baya ga rushe garuruwa fiye da 530, kuma tun daga wancan lokaci har kawo yanzu miliyoyin Falasɗinawa ke rayuwa a matsugunan wucin gadi ko sansanonin ƴan gudun hijira yayin da da dama ke rayuwa a ƙasashen maƙwabta bayan raba su da muhallan su.
Yayin yaƙin na watanni aƙalla 8 Isra’ila ta kashe dubban Falasɗinawa baya ga ƙwace aƙalla kashi 78 na Falasɗinu yayinda yankuna irin Yammacin gaɓar kogin Jordan da gabashin birnin Qudus da kuma Zirin Gaza kaɗai suka yi saura a hannun Labarawan yankin na Falasɗinu.
Bisa al’ada a irin wannan rana, Falasɗinawa kan yi taruka da tattaki har da zanga-zanga a wurare da dama don nuna baƙin cikin su ga abin da suka kira yunƙurin kawar da su da Isra’ila ta faro tun daga wancan lokacin, kuma har kawo yanzu ba ta sarara ba, yayin da suke ci gaba da neman haƙƙin su wajen ganin sun koma matsugunan su waɗanda ƙasar ta Yahudu ta ƙwace tun shekaru 78 da suka gabata.