Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wani mai suna Bala Yusuf dan karamar hukumar Dutse da ke jihar Jigawa da ake zargi da yinƙurin halaka wani direban mota tare da ƙoƙarin sace motar.


Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Bauchi, SP Nafiu Habib ne ya bayyana hakan, yana mai cewa wanda ake zargin ya umarci direban ya kai shi Jos daga Abuja, inda bayan isar su Jos, sai wanda ake zargin ya lallashi direban da nufin ya kai shi Bauchi domin ya ga iyala nshi.


Sanarwar ta ce, bayan sun isa Bauchi, sai mutumin ya sanyawa direban kwayoyin saka bacci a abinci, inda yayi yunkurin guduwa da motar, wadda aka kiyasta kudinta ya kai naira miliyan 5.


Ya ce, ’yan sanda sun kama wanda ake zargin tare da gano motar a hannunsa, sannan an kai wanda aka cutar Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.


Sanarwar ta kuma ce, ana ci gaba da bincike domin gano cikakken bayanin lamarin kafin gurfanar da shi a Kotu.