MAJALISAR NAJERIYA ZA TA FARA MUHAWARA KAN KUDIRIN KAFAR ‘YANSANDAN JIHOHI

Ana sa ran Majalisar Dattawan Najeriya za ta fara muhawara a yau Laraba kan wani muhimmin kudirin doka da ke neman samar da rundunonin ‘yansandan jihohi, wanda ake ganin zai kawo babban sauyi a tsarin tsaron ƙasar.

Kudirin gyaran Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika wa majalisar, zai bai wa jihohi 36 damar kafa da gudanar da rundunonin ‘yansandansu tare da ci gaba da kasancewar rundunar ‘yan sandan tarayya.

Tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999, gwamnatin tarayya ce ke da cikakken iko kan harkokin ‘yan sanda a faɗin ƙasar. Sai dai matsalolin tsaro da suka ƙaru a sassa daban-daban na ƙasar sun sa ake ci gaba da kira da a bai wa jihohi damar mallakar nasu rundunonin tsaro.

Kudirin ya sake tayar da muhawara kan fa’idoji da ƙalubalen samar da ‘yansandan jihohi a ƙasar da ke da yawan jama’a da bambance-bambancen ƙabila, addini da yankuna.