Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince da sanya dokar hana fita ta sa’o’i 16 a ƙananan hukumomi 10 na jihar domin magance matsalolin tsaro da ke addabar yankunan.

A wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Musibau Babatunde, ya fitar, an bayyana cewa dokar za ta fara aiki daga ranar Laraba, 24 ga Yuni, 2026, daga ƙarfe 4:00 na yamma zuwa ƙarfe 8:00 na safe.

Ƙananan hukumomin da dokar ta shafa sun haɗa da Oriire, Orelope, Irepo, Saki West, Saki East, Atisbo, Itesiwaju, Iseyin, Olorunsogo da Atiba, musamman yankunan da ke kusa da gandun dajin Old Oyo National Park.

Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne bayan zanga-zangar da ta ɓarke kan matsalar sace-sacen mutane, musamman bayan sace yara da malamai a yankin Oriire a watan Mayu. Masu zanga-zangar sun buƙaci gwamnati ta ƙara ɗaukar matakan gaggawa domin inganta tsaro da ceto waɗanda aka sace.