Jami’an Amurka sun sanar da samar da wata allurar rigakafin cutar Ebola ta gwaji yayin da ake ci gaba da fama da ɓarkewar cutar a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo (DR Congo).

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce ana jigilar maganin daga Amurka domin gudanar da gwaje-gwaje a asibitoci. Kamfanin Mapp Biopharmaceutical ne ya samar da allurar, wadda aka ƙera ta amfani da sanadaran garkuwar jiki daga mutanen da suka kamu da cutar Ebola amma suka warke a shekarar 2014.

Ana sa ran Hukumar Lafiya ta Duniya za ta gudanar da gwaje-gwaje domin tantance inganci da amincin maganin kafin a amince da amfani da shi.

A halin yanzu, babu wani magani ko allurar rigakafi da aka amince da ita don magance nau’in Ebola na Bundibugyo, wanda shi ne ya haifar da ɓarkewar cutar a yanzu, inda ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 250 tare da kamuwa da fiye da mutum 1,000.